Hukumar NSCDC ta kama mutane 29 bisa zargin hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Bauchi

NSCDC Mining

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC, ta tsare wasu mutane 29 da ake zargi da laifin hakar ma’adinai da yin barna ba bisa ka’ida ba a jihar Bauchi.

Kwamandan hukumar Oloyede Oyerinde ne ya bayyana haka ranar Asabar a Bauchi.

Ya ce ana gudanar da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kusa da madatsar ruwa ta Waya, mai tazarar kilomita 40 daga cikin birnin Bauchi.

Oyerinde ya ce, ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba suna haifar da zaizayar kasa, da mamaye filaye, da kuma barazana ga tsaro da ke shafar harkokin zamantakewa da tattalin arziki a yankin.

Kwamandan ya ce, a ranar 5 ga watan Janairu, rundunar da ke aiki da bayanan sirri ta kai wani samame a yankin inda ta kama mutane 29 da ake zargi a ranar 5 ga watan Janairu.

Karanta: ICPC ta kama tsohon hafsan sojan ruwa da kwamandan NSCDC bisa zargin zambar Naira Biliyan 3

Ya ce rundunar ta kwato babura uku, da ƙurar diban kasa guda shida da manyan cokulan diban kasa 15 da injina guda biyar, fartanya guda uku, gatari da bututun ruwa guda biyu da injin famfo ruwa daya.

Oyerinde ya ce jami’an ‘yan sandan sun kuma kama wani da ake zargi da laifin yin barna da kuma satar igiyar sulke a kabarin Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Ya ce jami’ansu sun kwato wata wayar hannu da guntuwar igiyoyin sulke da aka lalata.

Kwamandan ya jaddada kudirinsa na kare muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa tare da hana haramtattun ayyuka a jihar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here