Wani ma’aikacin filin jirgin sama, Auwal Ahmed Dankode ya mayar da dala 10,000 (Kimanin Naira miliyan 16) da aka samu a cikin wani jirgin sama yayin da yake tsaftace shi a Kano.
Dankode, ma’aikacin Kamfanin Kula da Jiragen Sama na Najeriya (NAHCO) ne, a lokacin da yake tsaftace jirgin a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, sai ya ga kudin.
Da yake zantawa da SolaceBase , Auwal Ahmed Dankode ya ce an gano kudin ne a wani jirgin saman kasar Masar da ya sauka da misalin karfe 1:30 na rana, Laraba.
‘’Ina gudanar da aikin tsaftace jirgin da ya sauka ne sai na ga kudin a cikin ambulan.
Dankode da ya gano kudaden, ya ce a bisa horon da suka yi, duk lokacin da suka samu wani abu a cikin jirgin, ana sa ran su kai rahoto ga mai kula da su.
A cewarsa, bayan ‘yan mintoci, mai kudin, wani mutum ya garzaya zuwa jirgin, domin neman kudin.
Ya lura cewa magidancin ya tambayi mutumin abin da yake nema, inda ya amsa da cewa kudi ne a cikin ambulan da ya manta a kujerar sa, wato lambar kujerar da aka samu kudin.
‘’ An yi wa mutumin tambayoyi da dama wadanda ya amsa da kyau kuma daga baya aka sako masa kudin.
‘’Mutane da yawa a filin jirgin sun dauke ni kafada suna yaba ni bisa wannan aikin alheri.
”Gaskiya na ji dadi sosai da farin ciki da har na yi wuya in kwanta barci a yanzu, domin ina farin ciki da cewa Allah ya yi amfani da ni don faranta wa wani rai.”
‘’Mayar da abin da ba nawa ba ga mai hakki ba komai ba ne a gare ni domin horon da muka samu daga gida kenan.
Amma ina jin dadi da na san kimar kuma mai shi wanda bai jin Hausa da Larabci ya yi farin ciki har ya rungume ni sau da yawa.’’.
Auwal wanda dan asalin garin Kode ne a karamar hukumar Bunkure a jihar Kano, ya shahara da tsananin tsoron Allah da gaskiya.