Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin karrama mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar Kano da suka rasu yayin da suke kan aiki, saboda gagarumar gudummawar da suka bayar wajen hidimar jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, inda gwamnan ya bayyana hakan a yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 36 da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Ismail Jibril Falgore, ya gabatar da kundin hasashen kasafin kudin shekarar 2026 ga gwamnan domin amincewa da shi a bangaren zartarwa.
Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga shugabancin Majalisar Dokokin Jiha, iyalan ’yan majalisar da suka rasu, da kuma al’ummar Jihar Kano baki daya, bisa rasuwar Hon. Aminu Sa’adu Ungogo daga mazabar Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji daga mazabar karamar hukumar Birni.
Gwamnan ya jaddada cewa gudummawar karshe da Hon. Aminu Sa’adu Ungogo ya bayar wa jihar ita ce jajircewarsa wajen kammala aikin hasashen kasafin kudin 2026, tare da tabbatar da shirinsa domin amincewar majalisa kafin rasuwarsa.
Yayin zaman, an gudanar da addu’o’i na musamman domin rokon rahamar Allah ga rayukan ’yan majalisar da suka rasu, inda kwamishinan harkokin addini, Sheikh Tijjani Auwal, da kwamishinan ilimi, Hon. Haruna Ali Makoda, suka jagoranci addu’o’in.
Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na tallafa wa iyalan marigayan, tare da tabbatar da dorewar gadon ayyukan majalisa da suka bari, ta hanyar aiwatar da kasafin kudin shekarar 2026 yadda ya kamata.













































