ICPC ta kama tsohon hafsan sojan ruwa da kwamandan NSCDC bisa zargin zambar Naira Biliyan 3

ICPC Operatives

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta kama Adam Imam Yusuf, mataimakin kwamandan hukumar tsaro na farin kaya (NSCDC) a jihar Kogi, bisa zargin karkatar da sama da naira biliyan uku.

Yusuf, wanda har ya zuwa yanzu, ana tsare da shi ne bayan kama shi daga gidansa na Gwagwalada Abuja, kuma zai fuskanci tuhuma.

Binciken da ICPC ta gudanar ya nuna cewa tsohon hafsan hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Usman Jibrin mai ritaya ne ya shirya wannan zamba ta hannun Yusuf da tsohon Birgediya Janar Ishaya Bauka Gangum mai ritaya.

Karin karatu: Obasanjo ya bayyana yadda hukumar ICPC da EFCC suka taimaka wa Najeriya Samun rangwamen bashi

Rahotanni sun ce shirin da ake zargin ya hada da karkatar da kudaden jama’a ta hanyar amfani da wasu kamfanoni na bogi guda 92 wadanda ba su da rajista da hukumar kula da kamfanoni (CAC).

Wani bincike da ICPC ta gudanar ya gano wadannan kudade zuwa ga Lahab Integrated, Gate Coast Properties, da wasu kamfanoni masu alaka, wanda ya kai ga samun sama da kadarori 18, ciki har da gidajen mai.

Hudu daga cikin wadannan kadarorin an kwace wa gwamnati kawo yanzu, yayin da ake ci gaba da shari’a kan sauran kadarorin, haka kuma ICPC na kara zage damtse wajen damke sauran wadanda ake zargi gaba daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here