Cibiyar nazari da gudanarwa ta ƙasa (Chartered), reshen Kano, ta karrama shugaban Jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u, Kano (KHAIRUN), Farfesa Abdulrashid Garba, bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar da yake bayarwa ga ayyukan cibiyar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen gudanarwa da kasuwanci Bilal Dahiru Tijjani ta bayyana hakan a ranar Lahadi.
Karin labari: Jami’ar KHAIRUN ta jaddada kudirinta na bada ilimi mai inganci cikin sauki ga sabbin dalibanta da sauran dalibai
A cewar sanarwar, Farfesa Garba ya bayyana karramawar a matsayin wani abin da zai sa a ci gaba da bayar da gudunmawa ga cibiyar da kuma ci gaban al’umma.
“Na yaba da wannan karramawa, kuma hakan zai kara min kwarin gwiwa wajen tallafawa Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya da kuma inganta nagartar ilimi,” in ji shi.
Ya kuma kara jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen samun nasarar ci gaba da gudanar da harkokin hukumomi, yana mai cewa, “Karfin jagoranci da hada kai su ne jigon samun sakamako mai kyau.