Wani Dan sanda ya kashe kansa a jihar Neja

Police badge

Wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda a jihar Neja, Shafi’u Bawa, ya kashe kansa a ranar Asabar, 8 ga Fabrairu, 2025.

An samu Bawa a rataye a saman rufin ne lokacin da mahaifinsa ya shiga dakin, bayan da ‘yan sanda suka dauke gawarsa zuwa asibiti.

An tabbatar da mutuwar jami’in a wani babban asibiti dake karamar hukumar Kontagora a jihar.

Karin karatu: Haɗarin mota ya kashe mutane 28 sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Vanguard, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Neja Sufeto Wasiu Abiodun, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa Bawa ya kashe kansa ba.

“A ranar 8/2/2025 da misalin karfe 2 na rana, mun samu rahoton cewa wani ASP Shafiu Bawah da ke unguwar Kotangora 61 ya kashe kansa ta hanyar rataye kansa a saman rufi saboda wani dalili da har yanzu ba a tantance ba.

“An cire gawar aka mika ga iyalan sa domin a yi masa jana’iza, kuma muna gudanar da bincike don gano dalilin daukar wannan lamarin,” in ji Wasiu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here