Kano za ta bunkasa masana’antar fata, don yin gogayya da na Turai – Sagagi

Abba Kabir Yusuf 1 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta baiwa masu sana’ar hannu a jihar tabbacin aniyar gwamnati na inganta sana’o’insu da kuma habaka tattalin arziki.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa kwamishinan kasuwanci, zuba jari da masana’antu na jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi wannan alkawarin ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin wata ziyara da ya kai garin Chiromawa da Kofar Wambai da ke karamar hukumar Birni, inda ya duba ayyukan masu sana’ar takalmi da jakunkuna, da kuma sana’ar fatun gargajiya.

Da yake jawabi yayin ziyarar, kwamishinan ya ce ya je yankin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya lura da yadda mata suka taka rawa wajen sana’ar fata a lokacin yakin neman zabe.

Sagagi ya bayyana cewa gwamnati na da burin inganta dkayayyakin don ba da damar fitar da su zuwa kasuwannin Turai.

Karin karatu: Gwamnatin Kano na shirin daidaita kasuwanni don inganta kudaden shiga

Ya kara da cewa ma’aikatar sa za ta shawarci gwamnan kan tallafin da ya kamata, ko ta hanyar injina, ko cibiyoyin hada-hadar jama’a, ko kuma jari.

A yayin ziyarar, kwamishinan ya kuma zagaya Majema da ke sana’ar sayar da fatun gargajiya, inda ya saurari matsalolin masu fatu na yankin.

Masu sana’o’in hannu da suka hada da matasa da mata, sun bayyana jin dadinsu da ziyarar da kuma kokarin gwamnati.

Sai dai daya daga cikin matan da ta nemi a sakaya sunanta, ta bukaci gwamnati da ta tabbatar da taimakon ya je musu kai tsaye, inda ta yi zargin cewa masu shiga tsakani na hana su tallafi.

“Amma muna kira ga gwamnati da ta ba mu tallafin kai tsaye saboda wadanda ke wakiltar mu ba sa ba mu,” in ji ta.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnati na tallafawa masana’antar fata a matsayin wani bangare na ci gaban tattalin arzikinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here