Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar, wanda nadin zai fara aiki daga ranar Litinin 10 ga Fabrairun 2025.
An sanar da nadin ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar, inda ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa gogewa da jajircewa da yake da shi, wadanda ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kudirin gwamnati da kuma ci gaba da sa jihar nan a kan manufofinta.
Umar Farouk Ibrahim ya shafe fiye da shekaru talatin yana hidima a gwamnati.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa a lokacin da ya ke aikin gwamnati tun daga shekarar 1987 zuwa 2023, ya samu wasu muhimman mukamai na shugabanci wadanda suka bayar da gudunmawa sosai wajen gudanar da mulki da tsarin gudanarwa na jihar Kano.
Daga watan Maris 2001 zuwa Mayun 2015, Ibrahim ya yi aiki a matsayin babban sakataren bincike da harkokin siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jiha, kuma da wannan matsayi nasa ya bada gudunmawa wajen dabarun tafiyar da ma’aikatun gwamnati.
Sabon Labari: Gwamna Yusuf ya nada sabon Sakataren gwamnati
Bayan haka, daga watan Yunin 2015 zuwa Maris 2016, Ibrahim ya rike mukamin babban sakatare a hukumar gudanarwa da ayyuka ta kasa baki daya, ya kuma taba rike mukamin sakataren gwamnatin jiha a lokacin hutun shekara a shekarar 2013 da 2014, inda ya nuna amana da gaskiya da shugabannin jihar suka ba shi.
Sabon Sakataren gwamnatin ya yi aiki a matsayin Sakatare na manyan kwamitoci da dama, da suka hada da kwamitin gudanar da harkokin wuta mai zaman kanta (2012-2015), Kwamitin tantancewa da sayar da kadarorin gwamnati a 2012, da kuma kwamitin tsare-tsare na biyan Kuɗi na Jiha (2000-2004).
Ana dai kallon nadin nasa a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa tsarin gudanarwar gwamnati mai ci da kuma saukaka aiwatar da manufofinta da shirye-shiryenta yadda ya kamata.
Gwamna Yusuf ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa nadin Ibrahim zai taimaka matuka gaya wajen tabbatar da manufofin gwamnatinsa ga jihar Kano, inda ya jaddada mahimmancin gogaggun jagorori wajen tafiyar da jihar don samun ci gaba mai dorewa.