Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance, lamarin da ya haifar da babban sauyi a siyasar jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da sauya shekar tasa ne a wani taro da aka gudanar a dakin taron Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Jihar Kano, inda ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da muradun al’ummar jihar.
Ya jaddada cewa manufar komawarsa jam’iyyar APC ita ce ƙarfafa haɗin kai, kwanciyar hankali da kuma hanzarta cigaban Jihar Kano, tare da tabbatar da cewa bayar da kyakkyawan shugabanci da amfanin dimokuraɗiyya ga al’umma ne babban fifikonsa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa, ciki har da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma Sanata Kawu Sumaila.
Karanta: Ɗan Kwankwaso ya yi murabus daga mukamin Kwamishinan Matasa
Haka kuma, mambobin majalisar zartarwar Jihar Kano, shugabannin jam’iyyar da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci taron, lamarin da ya nuna muhimmancin wannan sauyi a siyasar jihar.
Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da ake sa ran zai yi tasiri mai zurfi ga tsarin siyasa da daidaiton ƙarfi a Jihar Kano da ma yankin Arewa gaba ɗaya.













































