Kungiyar Mata ‘Yan Jaridu Ta Kasa Ta Karrama Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano

IMG 20240912 WA0082 1080x710

Kungiyar Mata ‘Yan Jaridu ta kasa (NAWOJ) ta karrama Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano Muhuyi Magaji Rimin gado da babbar lambar yabo, la’akari da irin namijin kokarin da yake yi na ganin Kano ta zama jihar da ba ta da cin hanci da rashawa.

A cewar shugabar kungiyar NAWOJ ta kasa Hajia Aisha Ibrahim, wannan karramawar wata shaida ce da ke nuna irin jajircewar da yake wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Tun da farko da take nata jawabin, Sakatariyar kungiyar NAWOJ ta kasa ‘Yar Asalin Kano, Hajia Wasila Ibrahim Ladan, ta yabawa Muhuyi Rimin Gado bisa matakan da yake dauka wajan fatattakar cin hanci da rashawa.

Ladan ta bayyana Muhuyi a matsayin jajirtacce mai kwazo da sanin aiki, wanda ke da suffofin shugabanci wanda a irin zaman sa kan karagar mulki, al’amuran cin hanci da rashawa za su yi karanci.

“Hakika kokarin Muhuyi ya yi tasiri sosai a jihar Kano, kuma karramawar da NAWOJ ta yi masa nada alaka irin kwarewa da gogewar sa wajan aiwatar da aiki”.

“Sannan aiki da yake na ba-sani-ba-sabo ya tabbatar da amanar sa, a salon gudanar da aiki wanda hakan ke jefa razani ga ma’aikatan gwamnati, wannan tsarin nasa tabbas ya zaburar da sabbin shugabannin da za su biyo sahunsa”. Acewar Ladan

Sakatariyar kungiyar ta jaddada cewa karrama Rimin Gado wata shaida ce da ke nuna irin kyakkyawar alakarsa da hukumomin gwamnati da kungiyoyin fararen hula wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Wasila ta na mai cewa irin wannan matakai da shugaban ke dauka na nuna gaskiyar sa karara wajan tunkarar murkushe ta’adar cin hanci da rashawa da ke dabaibaye cigaban kowacce alumma.

“Da yake shugaba ne masanin shari’a mutum na mutane, ya na sahun gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma tabbas jihar Kano na kan gwadabe zama abin koyi a fagen shugabanci na gari”. A cewarta

Hakazalika Shugabancin Nawoj ya baiwa Baba Halilu Dantiye, Kwamishinan ma’aikatar yada labarai lambar girmamawa la’akari da jajircewarsa wajen fito da manufofi, aikace-aikace da irin cigaban da ake samu a sassa daban-daban na gwamnati, wanda hakan ya sa jihohi da dama ke rige-rige domin kwaikwayon jihar kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here