Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka ya fice daga PDP

Osita Chidoka 720x430

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya yi murabus daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A ranar Juma’a ne Chidoka ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa a lokacin da ya fito a wani shiri na Politics Today a gidan talabijin na Channels.

Tsohon ministan ya ce ya rubuta wa mazabarsa da ke jihar Anambra kan matakin da ya dauka.
Chidoka ya ce zai sadaukar da lokacinsa ga Cibiyar Athena, wata kungiya mai zaman kanta (NGO) da ke da niyyar inganta manufofin jama’a da jagoranci a fadin Najeriya.

“Zan bar siyasa na wani lokaci. Ina mai da hankali kan Cibiyar Athena,” in ji Chidoka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here