Ɗan Kwankwaso ya yi murabus daga mukamin Kwamishinan Matasa

WhatsApp Image 2026 01 26 at 16.24.37 750x430 (1)

Mustapha Kwankwaso, ɗan jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa na Kwamishinan Matasa da Ci gaban Wasanni, tare da ficewa daga Majalisar Zartarwar Jihar Kano.

A cikin sanarwar murabus ɗinsa da ya fitar a ranar Litinin, Mustapha Kwankwaso ya ce ya ɗauki wannan mataki ne da “nauyin zuciya,” inda ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar Jihar Kano hidima.

“Ina miƙa godiyata ta musamman ga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba ni na yi wa al’ummar Jihar Kano hidima. Na amfana ƙwarai da ƙwarewa da darussan da na koya a lokacin da nake kan wannan muƙami, kuma ina godiya da amincewar da aka nuna mini,” in ji shi.

Tsohon kwamishinan ya kuma roƙi da a ci gaba da bai wa matasan Jihar Kano kulawa da goyon bayan da suka dace da su.

“Yayin da nake barin wannan muƙami, ina addu’ar matasan Jihar Kano su ci gaba da samun kulawa da tallafin da suka dace da su,” in ji shi.

Ya bayyana cewa lokacin da ya yi a ofis ya ba shi ƙwarewa mai muhimmanci, tare da gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa.

Hakazalika, ya yi addu’ar a ci gaba da saka hannun jari wajen ƙarfafa matasa da bunƙasa harkar wasanni a jihar.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa wannan murabus na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a yau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here