Wasu mutane 5 ‘yan asalin birnin tarayya Abuja sun ɓuƙaci kotu ta dakatar da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da ake shirin yi cikin kwanaki 17 masu zuwa. Masu shigar da ƙarar dai sun buƙaci a hana alƙalin alƙalai na ƙasar, mai shari’a Olukayode Ariwoola ko wani daga cikin masu iko daga rantsar da kowane ɗan takara ne da ya yi takarar shugabancin ƙasa a zaɓen da ya gabata na ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara.
Mutanen sun kuma bayyana cewa mazauna birnin na tarayya na da ‘yancin sanin cewa ko wanda za’a rantsar ya cika sharaɗin samun aƙalla kaso 25 na ƙuri’un da aka kaɗa a birnin tarayya Abuja.
Dokar ta sashe na 134(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya wacce ta ke cewa ba ma za a sanar da cewa wani ɗan takara ya lashe zaɓe ba har sai ya samu aƙalla kaso 25 na ƙuri’un da aka kaɗa a yankin birnin na tarayya.
Haka nan doƙar ta ƙara da cewa ba za a rantsar da mutum ba har sai ya cika wannan sharaɗi na samun kaso 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a Abuja. Haka nan kuma dokar ta jaddada cewa babu wani ɗan takara da za a rantsar a matsayin kwamandan askarawan Najeriya har sai ya kasance ya na da kaso 25 cikin 100 na ƙuri’un Abuja.
Baya ga haka masu ƙarar sun dogara da sashe na 135(1) da ke cewa muddun ba a samu wani daga cikin ‘yan takara da ya cika sharuɗan da doka ta tanada na a rantsar da shi ba, to shugaban ƙasar da ke kai zai ci gaba da riƙe ƙasar.
Sannan kuma sun dogara da dokar da ke cewa babu bayar da satifiket ko kuma gudanar da rantsuwar sabon shugaba har sai dai idan doka ta tabbatar da cewa ya cika duka sharuɗan da aka gindaya.
Sunayen mutanen da suka shigar da ƙarar waɗanda kuma suka kira kansu a matsayin ‘yan Abuja masu rajistar katin zaɓe sune: Anyaegbunam Okoye, David Adzer, Jeffery Ucheh, Osang Paul da Chibuike Nwachukwu. Mutanen dai sun ambaci sunan ministan shari’a na ƙasa da kuma sunan alƙalin alƙalai a cikin takardar ƙarar.