Rahotanni daga jihar Oyo na nuni da cewa mummunan fashewar abubuwa a wata tashar sayar da iskar gas ta auku a unguwar Sango da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa fashewar ta furgita mazauna garin tare da neman tsira.
Karanta wannan: ’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesan Jami’ar Ibadan
An samu hayaniya da misalin karfe 8:00 na dare, inda aka yi ta ratsa sassan birnin Ibadan har zuwa Bashorun da Amuda Ojeere a kan babbar hanyar Legaa saga Ibadan.
A cewar mazauna yankin shahararriyar Kasuwar Ace Mall da kuma gidan sinima na Ventura da ke Samonda wadanda ke da nisan mil dari daga wurin da aka samu fashewar a Sango ya ruguje.
Karanta wannan: KUST ta musanta karbar alawus na Naira Biliyan 1 daga Gwamnatin Kano
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba a san adadin wadanda suka mutu ba.