kungiyar Kasham Girls Women Youth and Community Development Network ta ja hankalin al’ummar jihar Kano da su kauracewa duk wani abu da zai kawo cin zarafin mata yayin zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi da za’a gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Dinatu Emmanuel Ishaku, ita ce tayi kiran a wani taron manema labarai da kungiyar ta kirawo ranar Alhamis a jihar Kano.
“A matsayin mu na kungiya mai zaman kanta, muna kira da babbar murya, tare da jan kunne ga matasa, da su kauracewa yin duk wani abu da zai kawo hargitsi, ko tashin hankalin wanda ka iya kai wa ga cin zarafin mata ya yin gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi a jihar Kano.”
Shugabar kungiyar ta kuma kara da cewa “martaba da darajar jihar Kano tana hannun mu, mu bar yan uwana mu yan mata da iyayen mu mata tsofaffi da su fito su kada kuri’ar su cikin kwanciyar hankali da lumina, ba tare da fargaba ba ko tashin hankali.”










































