Ministan Harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bukaci sanya wata ranar don amsa gayyatar da kotun da’ar ma’aikata (CCB) ta yi masa kan wani bincike da ake yi bisa zargin karya ka’idojin da’ar jami’an gwamnati.
Idan za a iya tunawa, a ranar Talata ne aka tsammaci ministan zai je hedikwatar CCB dake Abuja da misalin karfe 11 na safe domin amsa tambayoyi.
Karanta wannan: Ministan harkokin wajen Iran ya goyi bayan Houthi kan hare-haren da suke kai wa
Sai dai Tunji-Ojo bai je ofishin ba, inda ya aike da takarda ga hukumar wadda ta yi nuni da yana wajen wani aikin al’ummar kasa.
Amma dai wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa ministan ya yi watsi da gayyatar da CCB ta yi masa ne.
To amma a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta CCB, Veronica Kato, ta fitar ta ce za a sake sanya ranar da ministan zai gurfana a gabanta, sakamakon takardar da ya aike mata.
Hukumar CCB dai ta gayyaci ministan ne kan yadda kamfaninsa ya yi wata kwangila ta Naira miliyan 438 karkashin ma’aikatar jin kai da yaki da abkuwar ibtila’i.
Karanta wannan: INEC ta shirya gudanar da zaben cike gurbi a Kano–Kwamishinan Zabe
Kamfanin, New Planet Projects, da ake zargin na ministan ne, na daga cikin kamfanonin da suka ci gajiyar kwangilar da ma’aikatar ta yi.













































