Ministan harkokin wajen Iran ya goyi bayan Houthi kan hare-haren da suke kai wa

Minista
Minista

Wani abin dubawa shi ne yadda Amurka da Burtaniya ke zargin cewa Iran ce ke goyon bayan duk wasu hare-hare da ‘yan tawayen Houthi ke kaiwa jiragen kasuwanci a ruwan maliya.

Idan har mutum ya san wannan zancen to ba zai yi mamaki ba da kalaman ministan harkokin wajen Iran na nuna jin daɗinsa game da matakan Houthi kan Isra’ila a ruwan maliya, yana cewa Yemen ce ke da hakkin kare mashigar ruwan.

Karanta wannan: Majalisar Wakilan Amurka za ta fara shirin tsige shugaba Joe Biden

Hossein Amir-Abdollahian ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Yemen ta ɗauki matakin kare mata da ƙananan yaran da ake kashewa a Gaza, tare da nuna adawa da kisan ƙare dangin da take a Gaza.

Karanta wannan: Ana ci gaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasar Bangladesh

Ya kuma yi kira ga Amurka ta gaggauta daina goyon bayan Isra’ila – maimakon harin da take kaiwa Yemen – domin zaman lafiya ya dawo a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here