Tinubu da Kashim ba su yi katsalandan a Kotun Koli ba-Abba Kabir

Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430
Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kan rashin tsoma baki a hukuncin kotun koli.

Gwamna Yusuf ya ce shugaban kasar da mataimakinsa duk da matsin lamba daga wasu mutane, amma sun ki yin katsalandan a cikin hukuncin da ya ba shi nasara.

Karanta wannanWilliam Lai ya lashe zaben shugaban Kasar Taiwan

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Juma’a ne kotun koli ta tabbatar wa da Abba Kabir Yusuf nasara.

Gwamnan wanda ke cike da farin ciki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun kolin da ke Abuja ranar Juma’a.

Karanta wannan: Gwamnan Kano Yusuf da Gwamnan Bauchi Bala sun isa kotun koli gabanin yanke hukunci

Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na gidan gwamnatin Kano Aliyu Yusuf ya fitar a ranar Asabar, ta ce Abba ya kuma yabawa shugabannin jam’iyyar NNPP na kowane mataki, musamman jagoran tafiyar Kwankwasiyya ta duniya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa jagorancin da ya yi har aka kai ga nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here