Gawuna Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli, Ya Yiwa Abba Fatan Alheri

Kano Deputy Gov. Nasiru Yusuf Gawuna.jpeg
Kano Deputy Gov. Nasiru Yusuf Gawuna.jpeg

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar All Progressives Congress, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya amince da hukuncin kotun koli tare da taya Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC a ranar Juma’a a Abuja.

Gawuna ya ce ba shi da adawa da hukuncin kotunkoli, don haka ya bukaci Gwamna Yusuf ya yi wa al’ummar Kano hidima cikin adalci da gaskiya.
“Ina so in yi kira ga magoya bayana da su fahimci cewa duk abin da ya faru shirin Allah ne. Su kwantar da hankalinsu, su amince da hukuncin.”

“Jam’iyyarmu ta bi tsarin doka don kalubalantar zaben. Mun yi nasara a kotun koli da kotun daukaka kara, amma kotun koli ta yanke mana hukunci, don haka muna mutunta hukuncin. Kuma kun san cewa na taya shi murna kafin mu je kotu, kuma ina yi masa fatan alheri. Ina rokon Allah ya yi masa jagora a cikin shugabancinsa.”

“Ina kira ga mutanen jihar Kano nagari da su kiyaye doka da oda, kuma su ci gaba da yi wa jiharmu da kasarmu addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Ya kuma yi addu’ar Allah ya yi masa jagora a kan duk abin da zai yi ko kuma ya shirya yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here