Cikin Hotuna: Tinubu, El-Ruai, Gbajabiamila da wasu a Landan

Tinubu
Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya isa birnin Landan na kasar Birtaniya gabanin “laccar da zai gabatar a gidan Chatham ranar Litinin”, a cewar Jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Legas cikin Hotunan na tare da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila; Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru; tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; da sauransu.

Tinubu, mai shekaru 70, ana sa ran zai yi jawabi kan harkokin tsaro, tattalin arziki da kuma manufofin kasashen waje.

Tinubu yana takarar shugabancin kasa ne na shekarar 2023 tare da ‘yan takara na kan gaba da suka hada da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), Sen. Rabiu kwankwaso (NNPP) da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here