Hukuncin kotun koli: Sarkin Kano ya taya gwamna Abba Murna

Abba Kabir Yusuf and Aminu Ado Bayero 750x430
Abba Kabir Yusuf and Aminu Ado Bayero 750x430

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya taya gwamna Abba Kabir, murnar samun nasara a hukuncin kotun koli.

Sarkin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar ta ya murna da mai magana da yamun masarautar Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya fitar a ranar Talata.

Karanta wannan: Tinubu Ya Rabawa Sababbin Ministocin Sa Mai’akatu

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Sarkin a cikin sanarwar ya bayyana cewa hukuncin da kotun kolin ta yi wata ‘yar manuniya ce dake haska sahihiyar dimokaradiyya a kasar nan tare da tabbatar da halastattun zababbu da suka cika sharudan zabe.

Ya kuma bukaci gwamnan da ya yi duk mai yiwu wa wajen ganin ya cika alkawuran da ya dauka a yakin nema zabe, tare da kawar da duk wasu bambance-bambance a yayin sauke nauyin da Allah ya dora masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here