Kwamitin hadin gwiwa na fasahar jiragen sama da jiragen sama ya bayyana zargin mayar da na’urar kashe gobara daga kwalejin fasahar jiragen sama ta Najeriya (NCAT) Zariya a matsayin karya kuma mara tushe.
Alhaji Suleiman Richifa, shugaban kwamatin hadin gwiwa ya bayyana hakan a ranar Litinin a Zariya yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai kwalejin.
Richifa ya ce ziyarar ta biyo bayan kudurin da aka cimma a zaman binciken kwamitin hadin gwiwa na ranar 26 ga watan Maris.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Jirgin Dana ya yi hatsari a Legas
Sauraron binciken ya samu halartar ministan sufurin jiragen sama da shugaban hukumar NCAT da sauran masu ruwa da tsaki a kan shirin mayar da na’urar kwaikwayo da na’urorin kashe gobara daga NCAT zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Sai dai Richifa ya ce kwamitin ya gamsu da abin da ya gani a kwalejin tare da yabawa kwalejin kan na’urorin da ta ke da su na zamani.
Karin labari: Hukumar NAHCON ta kayyade wa’adin jerin alhazan jihohin bana
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ba da himma wajen kawo sauyi a kwalejin domin karfafa harkar sufurin jiragen sama.
Tun da farko, Mista Joseph-Shaka Imaligwe, mukaddashin shugaban hukumar NCAT, ya yabawa kwamitin bisa wannan ziyarar, inda ya kara da cewa akwai kage-kage da karya game da jigilar kayan aiki daga kwalejin zuwa wani wuri da ba a sani ba.