Muna samun ci gaba a yaki da miyagun laifuka-Gwamnatin Katsina

Gov Radda
Gov Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta ce tana samun gagarumar nasara a yakin da take yi da masu aikata laifuka duk da harin da aka kai wa ‘yan kasuwa a karamar hukumar Danmusa.

Kwamishinan tsaro na cikin gida, Dakta Nasiru Muazu Danmusa ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ranar Asabar a Katsina.

Karanta wannan: Gwamnatin Katsina zata fara bincika kan badakalar daukar Malamai a fadin Jihar

Ya ce an samu gagarumin ci gaba a yaki da satar shanu da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka tun daga lokacin da suka karbi gwamnati.

Sai dai ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun sha wahala sosai a yayin harin saboda an kashe da yawa daga cikinsu.

Kazalika kwamishinan ya gargadi al’ummar yankin da su guji boye miyagun mutane, yana mai cewa duk wanda aka samu yana aikata hakan zai fuskanci hukunci.

Ya bukaci mazauna jihar da a kodayaushe su rinka bayar da muhimman bayanai ga jami’an tsaro da za su taimaka wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 100 kan shirin ciyar da ɗalibai

Kwamishinan ya kuma bukaci mazauna jihar da su kara himma wajen bawa jami’an tsaron da aka tura yankunansu hadin kai, yana mai cewa hakan zai kara musu kwarin gwiwa.

Haka kuma ya bukace su da su ci gaba da neman taimakon Allah domin kawo karshen matsalolin tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here