Tinubu ya amince da sakin Naira Biliyan 3 don tabbatar da tantance Rajistar ‘yan kasa

Bola, Tinubu, 'yan sanda, ranar
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sanda ta kasa.Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya...

A ranar Litinin din da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan kasa da su kara hakuri, inda ta yi gargadi kan hukuncin da kafafen yada labarai ke yi a binciken da ake yi na karkatar da Naira Miliyan 585 da tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaki da talauci, Dakta Betta Edu ta yi.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mista Bayo Onanuga, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga sabbin bayanai kan lamarin, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da sakin naira biliyan 3 domin tabbatar da rajistar ‘yan kasa karkashin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Karanta wannan: Gobara ta sanya Mutane 120 rasa gidajen su a Ilorin

An kirkiri wannan rajistar ne domin mika kudi da sauran shirye-shiryen zuba jari a karkashin Buhari.

Wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 18 ga watan Disambar 2023, daga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ta bayyana a yi amfani da Naira biliyan 3 daga asusun tallafi na Covid-19 don tabbatar da rajistar zamantakewa na ƙasa.

Sanarwar ta kara da cewa “Da fatan za’a sanar da shugaban kasa ya amince da kashe Naira biliyan 3 kacal, daga asusun tallafawa marasa lafiya na Covid-19 don tabbatar da rajistar na kasa.”

Karanta wannan: Sojoji sun kama wasu dilolin kwaya a Ogun tare da kin karbar cin hancin miliyan 12

Amma da yake magana kan batun a daren Litinin din da ta gabata, Onanuga ya ce, “Shugaban kasa ya umurci hukumar EFCC ta binciki ma’aikatar jin kai kuma duk wadannan al’amura suna kan bincike.

“Na tabbata EFCC ta ga wannan takarda daga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kuma suna yin wani abu game da wadannan binciken.

Ya kara da cewa, “Mu kyale su suyi aikinsu, kada mu yi bincike sau biyu a kan al’amarin daya ko kuma yanke hukunci a kafafen yada labarai kan lamarin da ake bincike. ‘Yan Najeriya su yi hakuri.

Karanta wannan: Yan bindiga sun sace tsohon shugaban ƴan sanda a Burkina Faso

“Idan EFCC ta kamala bincikensu, za su mika rahotonsu ga shugaban kasa wanda zai yi aiki da sakamakon binciken” A cewar Onanuga.

Wani dandali na yanar gizo ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da kawar da talauci da ke karkashin Betta Edu ta biya wani kamfani mallakin ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo jimillar Naira Miliyan 438.1.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin New Planet Project Limited, yana daya daga cikin masu ba da shawara da aka bayar da kwangilar Naira Biliyan 3 da ministar kwangilar rajistar al’umma ta kasa ta bayar.

Karanta wannan: T. Gwarzo – Hukuncin kotun Ƙolin Najeriya bai razana APC ba

Sun ce, sauran wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da Fabunmi Olanipekun & Co wanda ya samu Naira Miliyan 419.5, Vintsolve Global Consult kuma an biya shi Naira Miliyan 558.8, Periscope Consulting ya samu Naira Miliyan 277, Blue Trend Enterprise ya biya Naira Miliyan 277.8, Laitop Dynamics Interlink Services ya samu Naira Miliyan 277.

Kazalika an biya Memak Nigeria Limited Naira Miliyan 277, MC Van Management Consult Limited ya samu Naira Miliyan 275.8, Danzinger Nigeria Limited ya samu Naira Miliyan 275.8, sai Blue Trend Enterprises da ya samu Naira Miliyan 277.8.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here