Yan bindiga sun sace tsohon shugaban ƴan sanda a Burkina Faso

download (1)
download (1)

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace tsohon shugaban ƴan sandan Burkina Faso.

An dauki Lt Col Evrard Somda a gidansa da ke Ouagadougou, babban birnin ƙasar ranar Lahadi, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

An kori Mista Somda daga aiki a watan Oktoban bara, mako ɗaya bayan da aka tsare wasu jami’an ƴan sanda guda huɗu da zarginsu da yunkurin juyin mulki.

Karanta wannan: William Lai ya lashe zaben shugaban Kasar Taiwan

Ana samun batun garkuwa da mutane a baya-bayan nan a ƙasar da ke Yammacin Afrika.

An yi garkuwa da Sansan Anselme Kambou wani hamshakin attajiri na kusa da Mista Somda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here