Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, tace ta samu rahoton kifewar wani jirgin ruwa a karamar hukumar Borgu ta jihar.
Darakta Janar na hukumar Alhaji Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar litinin a Minna.
Karanta wannan: Hukumar NUC ta magantu kan Farfesoshin bogi a Jami’o’i
Yace hatsarin jirgin ya auku ne da tsakar ranar litinin, yana mai cewa jirgin ruwan ya taso ne daga Dugga Mashaya dake mazabar Dugga, inda ya nufi kasuwar Wara dake jihar Kebbi.
Yace jirgin mai dauke da adadin mutanen da ba su gaza 100 ba, makare yake da kayayyakin amfani da suka hada da hatsi da saurana su.
Karanta wannan: Gwamna Abba ya nada Ganduje a matsayin mamba na majalisar dattawan Kano
Acewarsa, har yanzu hukumar ba ta kai ga tantace adadin wadanda suka mutu da wadanda suka tsira a hatsarin ba.
Kawo lokacin rubuta wannan labara, yace yanzu haka gamayyar jami’an hukumar da na karamar hukumar da abin ya faru na ci gaba da aikin ceto.