‘Yan sanda sun haramta amfani da POS ko taransifa a ofisoshinsu

POS, 'yan sanda, transfer, amfani
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sake nanata batun nan na haramta amfani da na'urar cire kudi ta POS da duk wani nau'in tura kudi a zamanance wato 'bank...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake nanata batun nan na haramta amfani da na’urar cire kudi ta POS da duk wani nau’in tura kudi a zamanance wato ‘bank transfer‘ a cikin caji ofis da sauran ofisoshin ‘yan sanda a duk fadin kasar.
Hakan ya biyo bayan zarge-zargen da ke tasowa cewa ana hada-hadar kudi ta hanyar amfani da na’urar POS ko taransifa da sa hannun wasu bare-gurbin  ‘yan sanda.

Karin labari: “Abinda yasa na dawo shugabancin hukumar Hisbah” – Sheikh Daurawa

Wannan haramci dai na da nufin kare kima da martabar aikin ‘yan sanda da hana yunkurin karbar cin hanci a duk ofisoshin ‘yan sanda na kasar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce babban sufeton ‘yan sanda na kasa IGP Kayode Egbetokun ya ja kunnen masu aikata hakan cewa za su kuka da kansu idan aka kama su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here