Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta tabbatar da tashin wata gobara a kasuwar Panteka dake jihar.
Daraktan hukumar Paul Aboi, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin Labarai NAN a ranar Laraba.
Karanta wannan: Gobara ta sanya Mutane 120 rasa gidajen su a Ilorin
Yace gobarar ta kone Shashen ‘yan katako na kasuwar.
Ya kara da cewa hukumar ta samu kiran farko daga wajen wani mai suna Sadiq Muhammad tun da misalin karfe 1 na daren Talata, Lamarin da ya sanya suka garzaya kasuwar.
Kazalika yace sun kuma karbi wasu kiraye-kirayen daga baya.
Ya kuma ce babu wanda ya rasa rai ko jin rauni a sanadiyar gobarar.
Karanta wannan: Daliban jami’ar FUDMA da aka yi garkuwa da su sun shaki iskar yanci
A cewarsa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.
Shugaban sashen ‘yan katako na kasuwar Muhammad Abubakar, yace gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 da min mintuna 10 na daren Talata.
Sai dai har lokacin rubuta wannan labari yace ba’a kai ga tattara adadin as asarar da aka yi ba.













































