Mahaifiyar Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, Uwargida Grace Akeredolu ta rasu.
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan dMista Richard Olatunde ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce marigayiyar ta rasu “lafiya a cikin lokacin barcinta da sanyin safiyar yau Alhamis tana da shekaru 90.
Sanarwar ta ce “Ta rasu ta bar ‘ya’yanta, jikoki da sauran ‘yan uwa, Kuma nan gaba kadan za a fitar sabuwar sanarwa”













































