Gwamnatin tarayya ta musanta maganganun da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa ana kisan gillar Kiristoci a sassan Najeriya, inda ya sanya ƙasar cikin jerin “ƙasashe masu damuwa ta musamman.”
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin waje Kimiebi Ebienfa ya fitar a safiyar Asabar, gwamnati ta bayyana cewa zargin bai dace da hakikanin yanayin da ake ciki a ƙasar ba.
Sanarwar ta ce Kiristoci da Musulmai a Najeriya suna rayuwa tare cikin lumana tun tsawon lokaci suna aiki da yin ibada cikin fahimtar juna.
Gwamnatin ta nuna godiya ga damuwar duniya kan haƙƙin ɗan Adam da ’yancin addini, amma ta bayyana cewa bayanan da Trump ya dogara da su ba su da tushe.
Ta ce ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Tinubu, Najeriya ta kuduri aniyar yaki da ta’addanci, karfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da haƙƙin kowane ɗan ƙasa.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa cikin natsuwa da gwamnatin Amurka don ƙarfafa fahimtar juna game da al’amuran yankin da kuma kokarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
A daren Juma’a, shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya wallafa a dandalin sada zumunta na (Truth Social), inda daga bisani fadar White House ta sake wallafawa, cewa ya ayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai damuwa ta musamman” saboda abin da ya kira barazana ga Kiristanci a ƙasar.
Trump ya bayyana cewa Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya, yana mai cewa dubban Kiristoci ana kashe su kuma ’yan ta’addan Musulmai ne ke da alhakin hakan.
Ya umarci majalisar dokokin Amurka da ta duba batun tare da bayar da rahoto, yana mai cewa Amurka ba za ta zuba ido ba yayin da irin wannan ta’asa ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe.
A wani bangare, ministan yada labarai da daidaita al’adu Mohammed Idris, cikin wata hira da gidan talabijin na CNN, ya musanta cewa ’yan ta’addan Najeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai, yana mai cewa duka Musulmai da Kiristoci hare-haren na samun su musamman a yankin arewa.
A wani lamari mai nasaba da haka, kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar Turai ya kira taron manema labarai a Abuja inda ya bukaci ƙarfafa kariya ga al’umma masu rauni da tabbatar da gaskiya wajen shawo kan matsalolin tashin hankali a faɗin ƙasar.













































