Dakarun bataliya na 195, sashin na 1 na Operation Hadin Kai, tare da hadin guiwar jami’an tsaro farin farar hula, a ranar 5 ga watan Disamba, sun halaka ‘yan ta’ddan Boko Haram hudu a yankin Mafa na jihar Borno.
An tattaro yadda dakarun, suka yi amfani da wasu gamsassun bayanan sirri, gami da kai samame a maboyar ‘yan ta’addan cikin yankunan Karkut da Kashobe.
Wata majiyar sirri, kwararriya wajen bada bayanai game da hare-hare da hasashe kan tsaro a tafkin Chadi ya shaidawa Zagazola Makama yadda dakarun suka yi arba da ‘yan ta’addan a Karkut yayin da take bincike a Kezemari da Ladinbuta.
A cewarsa, bataliyar tare da hadin guiwar jami’an tsaron farar sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan, yayin da tsananin luguden wutar da suka yi ya janyo raunatawa gami da halaka hudu nan take yayin da sauran suka ranta a na kare.
Wasu majiyoyi sun bayyana yadda aka tarwatsa sabbin sansanoni har shida na ‘yan ta’addan yayin da aka gano abubuwa masu fashewa, makamai da wayoyi a yankin.
Kamar yadda ya bayyana, dakarun ‘yan sa kai, wadanda basu kyale komai haka nan ba yayin binciken, sun bincike kafatanin yankin, tare da tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda da dama.













































