Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 18 ga watan Fabrairu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Dr Peter Adamu, shugaban kungiyar ASUU reshen KASU ya fitar a ranar Litinin.
Adamu ya ce an dauki matakin dakatar da yajin aikin tun a ranar Asabar.
“Gwamnatin ta nuna farin cikinta wajen warware wannan matsala ta hanyar gaggauta sakin kudade domin biyan kashi 60 cikin 100 na albashin watan Satumba na 2017 da aka hana da kuma ba da alawus na kula da aikin horar da dalibai”.
Karin karatu: Jami’ar KWARA ta yi martani kan dakatarwar ilimin shari’a da JAMB tayi
Kungiyar ta bayyana jin dadin ta ga Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, bisa gaggawar sa tare da jagoranci wajen warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin.
Kungiyar ta kuma godewa mahukuntan jami’ar, kwamishinonin ilimi, wasanni, da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar da suke takawa wajen ganin an shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Adamu ya yi kira ga dukkan ma’aikatan ilimi da su koma bakin aiki tare da ci gaba da yi wa al’ummar jami’a ayyukan su na yau da kullum. (NAN)













































