By Aminu Madobi
Kwamitin karɓar ƙorafin zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Kano, ya ce, ya zuwa yammacin yau Litinin bai samu rahoton ƙorafi ko kuma rashin gamsuwa kan yadda aka gudanar da zaben ba a filin Wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar mata.
Shugaban Kwamitin da Jam’iyar ta APC ta tura shi jihar Dakta Tony Macfoy, ne ya bayyana hakan a wani taron Manema labarai da ya gudanar a shalkwatar jam’iyyar ta Kano.
Dakta Macfoy, ya ce, a zaman karɓar ƙorafe-ƙorafen da Kwamitin ya yi har na a tsawon kwanaki uku bai samu ko da ƙorafi guda ba.
”Mun yi zama na kusan kwanaki 3, Amma har yanzu babu ko mutum guda da ya zo domin ba mu Rahoton ko gabatar da ƙorafinsa.”
Sai dai shugaban kwamitin ya ce za su je hutun rabin Lokaci ,Inda zasu fara rubuta Rahotonsu don miƙa wa uwar jam’iyyar ta Kasa a birnin tarayya Abuja .
“Muna nan Kano tun ranar Asabar, Kuma duk wanda zai Kawo ƙorafi game da zaben a shirye muke mu karɓa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya tanada”.
Kwamitin mai mutane 5 ya fara zaman karɓar ƙorafe-ƙorafen ne tun ranar Asabar ɗin da ta gabata a shalkwatar jam’iyyar ta Kano da ke kan titin Maiduguri.
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin tsagin da suka ja tinga kan batun zaɓen shugabancin jam’iyar abun ya ci tura.













































