2027: Jam’iyyar APGA ta goyi bayan Tinubu a zaben shugaban kasa

Bola Tinubu and Charles Soludo 1

Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta bayyana goyon bayanta ga shugaba Bola Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Awka.

A cewarsa, jam’iyyar APGA da APC za su yi aiki tare a lokacin zaben, domin dukkanin jam’iyyun biyu na da ra’ayin ci gaba.

Karin karatu: Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

An bayyana hakan ne a dandalin Alex Ekwueme da ke Awka a ziyarar aiki da shugaban kasar ya kai jihar.

Soludo ya ce, “Masu son ci gaba suna aiki tare.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here