Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, wadda ta ba shi damar tasowa a siyasa har ya zama sanata sannan daga baya ya zama gwamna.
Adeleke ya bayyana haka ne a shafinsa na X da daren Litinin ce, inda ya haɗa wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da ranar 4 ga Nuwamba 2025 da ya tura zuwa shugaban jam’iyyar na gunduma ta 2 Sagba Abogunde a karamar hukumar Ede ta Arewa a jihar Osun.
A cikin wasiƙar, ya danganta matakin nasa da rikicin da ke ci gaba da addabar shugabancin jam’iyyar PDP a matakin ƙasa, wanda ya ce ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar nan take.
Ya bayyana godiyarsa ga PDP bisa damar da ta ba shi ya wakilci Osun ta Yamma a majalisar Dattawa daga 2017 zuwa 2019 sannan kuma ta ba shi damar zama gwamnan jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban gundumar ya karɓi wasiƙar murabus ɗin nasa tun ranar 4 ga Nuwamba, sai dai Adeleke bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba bayan ficewarsa daga PDP.
Duk da cewa bai ambaci sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba, bayanai sun nuna cewa yana iya komawa jam’iyyar Accord a kwanaki masu zuwa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta ta ƙasa ta sa ranar 8 ga Agusta 2026 domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.
A tarihin siyasar Adeleke, ya lashe kujerar sanata ta Osun ta Yamma a zaben cike gurbi da aka gudanar a shekarar 2017.
An rantsar da Adeleke a ranar 27 ga Nuwamba 2022, bayan ya kayar da tsohon gwamna Gboyega Oyetola a zaɓen gwamna da aka yi ranar 16 ga Yuli 2022.
Ficewarsa daga jam’iyyar PDP a 2025 ya zama babban sauyi a siyasar jihar Osun, inda hakan ya tayar da tambayoyi kan matakin da zai ɗauka gabanin zaɓen gwamna na 2026.













































