Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya sake nada Ibrahim Kassim a matsayin sakataren gwamnatin jihar.
Rahotanni na nuni da cewa gwamnan ya baiwa Kassim mukamin ne amatsayin ladan hidimar biyayyar da ya yi masa, na janyewa da ga takarar gwamnan jihar bayan ya yi nasara a zaben fidda gwani, domin baiwa Kaura damar tsayawa takarar gwamnan a karo na biyu.
A baya bayan nan ne Gwamna Bala ya tsaya takarar neman shugaban kasa a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.













































