Gas ya jikkata mutane 20 tare da ƙone shaguna uku a kano

Fire marlet
Fire marlet

Tukunyar iskar gas ta kara fashewa a jihar Kano, inda shaguna uku suka ƙone tare da jikkata mutane 20.

Al-amarin ya faru ne jiya Alamis da misalin 8:30 na dare, a wani shagun da ake siyar da iskar gas mai suna  Liquefied Petroleum Gas a unguwar sheka karshin-kwalta.

Malam Abubakar, na daya daga cikin wadan da al-amarin yafaru a gaban su, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewa mutane da dama an garzaya dasu asubiti jikkunan su a kone, ya kara da cewa mafi yawan cin wadan da abin ya rutsa dasu, mutanan dake cikin shagun ne, sai kuma mutanan da ke gudanar da harkokin kasuwan cin su a kusa da shagun.

Kakakin hukamar kashe gobara ta jihar kano, Mallam Saminu Yusif ya tabbatar da faruwar al-amarin, inda yakara da cewa mutune 20 da hatsarin ya rutsa da su suna raye, yanzu haka suna karbar kulawa ta gaggawa a asibiti. Sanan ya ce ana zargin hadarin ya faru ne sakamakon wani mai suyar kifi a kusa da shagon da ake siyar da iskar gas din.

Idan za’a tunwa dai a ranar 17, ga watan 5, na shikarar 2022 Jaridar solacebase ta ruwaito cewa tukunyar gas ta fashe a unguwar sabon gari, inda mutum 4 suka rasa rayukansu, ya yin da dama suka jikka-ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here