Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta cafke wani jami’an sojan ruwa mai suna Ibrahim Adamu, mai shekara 25 a duniya da wani jami’in gandiroba mai suna Abdullahi Abdulwahab, mai shekara 26, bisa zargin fashi da makami. The Punch ta kawo rahoto cewa a na zargin jami’an guda biyu ne da aikata laifin fashi da makami da ƙwacen mota.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, yayin taso ƙeyar waɗanda ake zargin a ranar Talata, ya bayyana cewa jami’an su ne suka cafke su ne sanye da kayan sojoji a Ekpoma, biyo bayan samun bayanan sirri.
Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun farmaki direban motar ƙirar C300 Mercedes Benz wacce ba ta da rajista a Sapele, cikin jihar Delta, suka ƙwace motar daga hannun sa sannan suka tilasta masa tura mu su N400,000 a cikin asusun bankin su.
Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin suna shirin tafiya da motar ne birnin tarayya Abuja, lokacin da ƴan sanda suka cafke su a Ekpoma, cikin jihar Edo.
Kakakin ya kuma ƙara da cewa: “Waɗanda ake zargin sun bayar da bayanai inda suka yi iƙirarin cewa su jami’an sojin ruwa ne da gandiroba.”
Nwabuzor ya ce an kwato motar da kayan sojojin da su ke a hannun waɗanda ake zargin. Da ya ke magana da manema labarai, Ibrahim Adamu, wanda ya shiga aikin soja a shekarar 2019, ya ce an cafke shi ne bisa satar mota ƙirar Mercedes Benz C300 a jihar Delta.













































