Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Damaturu na jihar Yobe a ranar Laraba ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Fika ta Gabas da Jakusko.
Kotun da ke karkashin Mai shari’a Fadima Murtala ta bayyana rashin bin ka’idojin dokar zabe inda ta umarci jam’iyyar APC da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14.
Mai shari’a Fadima Murtala ta ce yanzu haka an baiwa jam’iyyar wa’adin kwanaki 14 ne kacal domin gudanar da sabon zaben fidda gwani na kujeru biyu da ba kowa ayanzu.
Har ila yau, a wani labarin makamancin haka, dan takarar kujerar Sanata a jihar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Abubakar Jinjiri ya janye karar da ya shigar kan dan takarar sanatan yankin Bashir Sheriff Machina, da hukumar zabe mai zaman kanta da kuma jam’iyyar APC kan bukatar sa, na Sanata.













































