Fusatattun matasa sun kashe mutane 3 da ake zargin suna kai wa ƴan bindiga bayanai

map of Kaduna state
map of Kaduna state

Gwamnatin jihar kaduna ta tabbatar hallaka wasu mutane uku da ake zargin masu bai wa ƴan ta’adda bayanan sirri ne, a yankin zangon Aya dake karamar hukumar Igabi.

Kwamiahinan tsaro da al’amuran cikin gida Samuel Aruwan, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, fusatattun matasan sun yiwa gidan mutanen da ake zargi tsinke, waɗanda kuma ake alaƙanta su da lefukan satar mutane da ke faruwa a yankin.

Mista Aruwan ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin Abdullahi gobirawa da matarsa  Binta Abdullahi da kuma ɗansu Hassan Abdullahi.

Kwamishinan ya ce, bayan hallaka mutanen, dandazon matasan sun wawashe kayayyakin su kafin daga bisani su banka wa gidan wuta.

Mista Aruwan ya ƙara da cewa, bayan samun rahoton Gwamna El’rufai ya bayyana ɓacin ransa game da ɗaukar wannan doka a hannu, inda ya yi Allah wadai da hakan.

Ya kuma ce, gwamnan ya buƙaci jami’an tsaro da su gudanar bincike kan lamarin tare da buƙatar jama’a da su cigaba da girmama doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here