Gwamnatin jihar Kano ta amince da kafa makarantar koyon aikin jinyar idanu a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan a ranar Talata a lokacin da yake bude taron wakilan kimiya na kasa da ayyukan kula da ido kyauta karo na 34 da kungiyar ma’aikatan jinya ido ta Najeriya ta shirya a gidan gwamnati dake Kano.
Ganduje wanda mataimakinsa, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana cewa kafa makarantar ya biyo bayan laákari da mahimmancin kula da ido ga ci gaban rayuwar dan Adam.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya fitar a ranar Talata kuma aka aika zuwa Solacebase.
A cewar Gwamna…”Gwamnatinmu ta ba da fifiko wajen samar da kiwon lafiya saboda ci gaban kowace al’umma yana da nasaba da ingantacciyar lafiya… don yin wannan aiki mun ware kashi 15% na kasafin kudin shekarar 2021 ga bangaren kiwon lafiya.
Taken taron na bana shine: “Binciko cigaban da aka samu duniya ta fannin aikin jinyar idanu, inda gwamnan ya bayyana shi a matsayin abu mai mahimmanci, kuma ya kara samun kaimi wajen ganin an bunkasa fannin jinyar idanu domin samun cigaba
A lokacin da yake yi wa kungiyar fatan samun nasarar taron, ya kuma ba su tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai.
A nasu jawabin shugaban kungiyar ma’aikatan jinya ta ido ta kasa da takwaran sa na jihar Kano Stephen Lamiya da Saleh Iliyasu Dan Hassan sun bayyana cewa taron wani gagarumin kokari ne na hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki daga matakin kananan hukumomi da jiha da kasa baki daya fannin likitanvin ido wanda ya fara a watan Nuwamba 2020.
Sun kara da cewa lura da mahimmancin idanu a rayuwar dan adamyana bukatar kula sosai, shiyasa ma suka yiwa taken taron na bana da cewa “Ku so idanunku”, inda suka yi kira ga masu jinyar idanu da sadaukar da kansu wajen aiki da kwarewarsu ga kasa.
Sauran wadanda suka yi jawabi a lokacin bikin sun hada da kwamishinan lafiya Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa, babban daraktan kula da lafiya na asibitin koyarwa na Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Sheshe da kuma Dokta Ado Shehu Ringim na jami’ar Maryam Abacha American University.













































