Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya kwace filaye mallakar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas; da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Haka kuma, dana wasu fitattun mutane 759 a Maitama II, Abuja. Haka kuma sokewar ta shafi rashin biyan takardar shaidar zama.
SolaceBase ta rahoto cewa a cikin sanarwar Wike ya fitar ranar Alhamis, Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta ce mutanen da abin ya shafa sun kasa biyan takardar shaidar (C-of-O) na filayen da aka kwace.