Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta shawarci ‘yan Najeriya da su rika siyan kaya a koda yaushe daga inda za su iya gano mai siyarwar da rasiti.
Darakta-Janar na hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ita ce ta ba da wannan shawarar a hirar ta da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Ta ce siyan kaya daga inda ake ba masu saye takardar, zai baiwa masu saye damar gano wurin a lokacin da kayan suke da lahani.