Jam’iyyun adawa ne ke tunzura jama’a su yi zanga-zanga – APC

Tinubu, bude, iyakoki, najeriya, nijar
Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar. Ya kuma dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan...

Jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta zargi jam’iyyun adawar kasar da ingiza matasa su hau kan tituna da sunan zanga-zanga kan abin da ta bayyana da nuna gwamnatin shugaba Tinubu da wannan ta gaza a tafiyar da mulki a kasar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar ta APC, Felix Morka ya fitar, jam’iyyar ta ce jerin zanga-zangar da aka yi a birnin Kano da Minna duka sun nuna irin zakuwar bangaren adawa na tunzura jama’a su yi wa gwamnati bore.

“Faruwar zanga-zangar a lokaci guda ba hakan nan ba. Alamu ne da ke nuni da kishirwar tayar da zaune tsaye domin yi wa gwamnati zagon kasa wanda kuma hakan ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa” in ji sanarwar.

Karanta wannan: Za’a ga yanayin hazo da kura na kwana uku a Najeriya – Nimet

Mista Felix ya kara da cewa a daidai lokacin da gwamnati ta amince ‘yan kasa su nuna damuwarsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya to amma su yi hakan ta hanyar da ta dace da kuma doka ta tanada sannan ka da su mika akalarsu ga ‘yan adawa da ke so yin amfani da su domin tayar da tarzoma.

Daga karshe sanarwar ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na sane da halin da ‘yan kasa ke ciki kuma tana yin duk abin da za ta yi wajen tabbatar da ta share musu hawaye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here