Za’a ga yanayin hazo da kura na kwana uku a Najeriya – Nimet

yanayi, hazo, kura, sanyi, najeriya, NImet
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun hazo da kura daga ranar Talata zuwa Alhamis a sassan kasar. A bayanin hasashen da hukumar ta fitar...

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun hazo da kura daga ranar Talata zuwa Alhamis a sassan kasar.

A bayanin hasashen da hukumar ta fitar ranar Litinin a Abuja, an yi hasashen samun kura da hazo mai tsanani da ka iya shafar tashi da saukar jiragen sama.

A cewar Nimet, ana sa ran ganin hazo da kura mai tsananin a jihohin arewa da arewa ta tsakiya.

Hukumar ta kara da cewa a ranar Alhamis za’a fuskanci raguwar yanayin na hazo da kura a jihohin yankunan biyu.

Karanta wannan: EFCC ta kama wani fasto bisa zargin damfarar Naira Biliyan 1.3

Nimet ta ce a jihohin kudancin Najeriya kuma, za’a ga sauyin yanayi a ranar Alhamis inda da safe za’a ga disashewar yanayi daga bisani kuma ya yi sauki.

Hukumar ta kuma ba da shawara a kula wurin sa wa yara kanana da tsofaffi kayan sanyi.

Ta kuma ce ya kamata jirage su duba yanayi da hasashen hukumar Nimet domin tsara yadda zirga-zirgarsu za ta kasance na iya ranakun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here