Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar Nnamdi Kanu na sauya masa gidan gyaran hali daga Sokoto

Nnamdi Kanu in Court 1

Kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari’a James Omotosho ta ƙi amincewa da buƙatar da shugaban haramtacciyar ƙungiyar Biafra, Nnamdi Kanu, ya gabatar domin a maida shi daga gidan gyaran hali na Sokoto zuwa wata cibiyar tsarewa da ke Abuja ko jihar Nasarawa.

Kanu, ta hannun hukumar bayar da taimakon lauya, ya roƙi kotun da ta bayar da umarni ga gwamnatin tarayya ko hukumar kula da gidajen gyaran hali su gaggauta maida shi zuwa cibiyar Kuje da ke Abuja ko ta Keffi da ke Nasarawa.

A madadin haka kuma, ya nemi a maida shi zuwa kowace cibiyar tsarewa da ke ƙarƙashin hurumin kotun, ciki har da Suleja ko Keffi, domin samun damar bin diddigin karar da yake shirin daukaka.

Sai dai a zaman da aka yi a ranar Litinin, mai shari’a James Omotosho ya ƙi amincewa da wannan buƙata, yana mai cewa ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba sai an ji amsar gwamnatin tarayya a matsayin ɓangare na adalci kafin kotu ta yanke hukunci.

Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa wajibi ne gwamnati da hukumar NCoS su samu cikakken sanarwa domin su yi nasu bayani kafin a ɗauki mataki kan wannan roƙo.

Karanta: An mayar da Nnamdi Kanu gidan yari a Sokoto – Lauya

Daga nan kotun ta dage sauraron buƙatar zuwa ranar 27 ga Janairu, 2026, domin ci gaba da shari’ar.

A ranar 20 ga Nuwamba, kotu ta same shi da laifuka guda bakwai da suka shafi ta’addanci da gwamnatin tarayya ta gabatar, inda ta yankewa Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Daga bisani aka tura shi gidan gyaran hali na Sokoto saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta a Kuje, inda aka taba samun harin da ya fasa gidan yari.

Lauyansa, Aloy Ejimakor, ya sake gabatar da wata buƙata a gaban mai shari’a James Omotosho yana neman a maida shi cibiyar tsarewa da ta fi kusa da Abuja, kamar ta Suleja ko Keffi.

A cikin buƙatar da Kanu ya sanya hannu da kansa, ya roƙi kotun ta amince a saurare shi ba tare da halartarsa ba, tare da neman gwamnati ta aiwatar da maida shi.

A cikin dalilan da ya gabatar, Kanu ya bayyana cewa nisan fiye da kilomita 700 daga Abuja zuwa Sokoto ya hana shi damar shirya takardun daukaka ƙara cikin sauƙi.

Ya ce dukkan mutanen da ke taimaka masa, iyalai, abokan hulɗa da masu ba shi shawara suna Abuja, lamarin da ya sa zama a Sokoto yake rage masa damar kare kansa yadda ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here