Mutum goma sun rasu a hatsarin mota a Kwara

1689444900679
1689444900679

Mutum goma goma ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Jebba-Bode a jihar Kwara.

Lamarin ya rutsa da mutum 17 waɗanda suka haɗa da maza 12 da mata guda biyu da kuma wasu yara guda uku.

Mutanen da suka mutu sun kunshi maza guda bakwai da mace guda ɗaya da kuma yara biyu.

Hatsarin ya afku a ranar yammacin ranar Alhamis, inda wasu motoci guda uku suka garu, abin da kuma aka danganta faruwarsa da gudu fiye da kima da kuma kokarin wucewa da direbobin motocin suka yi.

Babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar, Fredrick Ade Ogidan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa, yayin da aka kai waɗanda suka mutu kuma ɗakin ajiyar gawawwaki na asibitin koyarwa na Jami’ar jihar da ke Ilorin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here