Kotu ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan Ganduje

Court Gavel
Court Gavel

Babbar kotun tarayyar da ke Kano ta ba da umarnin a saki wani tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Idris Wada Saleh wanda ake zargi da almundahanar naira biliyan ɗaya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ne babbar kotun Majistaren jihar ta umarci tsare shi a hannun hukumar karɓar ƙorafe- ƙorafe hana cin hanci ta jihar Kano (KPCACC).

An zargi tsohon kwamishinan da yaudara da kuma yin karya a takardun wasu ayyuka zamanin gwamnatin da ta wuce.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi zargin cewa a 2023, tsohon kwamishinan ya bai wa kamfanin Arafat construction da ‘Multi resources’ kudi nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin jihar.

To sai dai in ji hukumar, babu ko ɗaya cikin ayyukan da aka yi. A baya-bayan nan dai hukumar KPCACC ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a kan ‘bidiyon dala’.

To amma babbar kotun tarayya a jihar ta dakatar da hukumar a kan wannan batu, har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙorafin da Ganduje ya shigar gabanta yana neman ta hana hukumar binciken sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here