Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Nairobi dake kasar Kenya domin halattar taron kungiyar kasashen Afirka AU.
Shugaban ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da kuma mai bashi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake.
Ana sa ran dawowar shugaban bayan kammala taron.