Wani hari da Isra’ila ta kai kudancin Lebanon ya halaka babban kwamandan kungiyar Hizbullah.
Wasu majiyoyin tsaro uku ne suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Karanta wannan: Kungiyar Hizbullah ta yi wa Isra’ila martani kan kisan Al-Arouri
An bayyana sunan kwamandan da Wissam Al-Tawii, mataimakin shugaban wani sansani cikin rundunar kungiyar ta Radwan, a cewar rahoton Reuters.
Reuters ta ce an kashe al-Tawii da wani dan kungiyar Hizbullah lokacin da hari ya shafi motarsu a kauyen Majdal Selm da ke Lebanon.
Karanta wannan: Sojin Isra’ila sun bayyana cewa suna gwabza kazamin fada a kudancin Gaza
Daya daga cikin majiyoyin tsaron ta ce “wannan hari ne mai matukar ciwo,”
Wata majiyar ta kara da cewa “Abubuwa za su ta’azzara yanzu.”
A baya, jagoran Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya gargadi Isra’ila ta guji kai hari kan Lebanon.